Wasanni

Wasanni

A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.

00:00
00:00

Zusammenfassung der Episode

Shirin 'Duniyar Wasanni' tare da Khamis Saleh zai maida hankali ne kan kyautar Ballon d’Or da aka bayar a ranar Litinin ɗin data gabata. Kyaftin ɗin tawagar Ingila Harry Kane ya lashe kyautar a bana, inda ya zamo ɗan wasan ƙasar na farko daya lashe ta cikin shekaru 25, wato tun bayan Michael Owen a shekarar 2001. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin...........

Folgen

686-

Sharhi akan kyautar Ballon d'Or ta 2026 wadda Harry Kane ya lashe

Shirin 'Duniyar Wasanni' tare da Khamis Saleh zai maida hankali ne kan kyautar Ballon d’Or da aka bayar a ranar Litinin ɗin data gabata. Kyaftin ɗin tawagar Ingila Harry Kane ya lashe kyautar a bana, inda ya zamo ɗan wasan ƙasar na farko daya lashe ta cikin shekaru 25, wato tun bayan Michael Owen a shekarar 2001. Ku latsa alamar sauti don sauraron shirin...........

02 Nov. 2026
685-

Sharhi kan yadda ta kaya a wasan El-Clasico da aka yi a ƙarshen mako

Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako ya maida hankali kan wasan El-Clasico da aka yi tsakanin Barcelona da Real Madrid. Shi dai wasa tsakanin waɗannan ƙungiyoyi ba wai wasa bane na gama gari, domin yanada ɗinbin tarihi ganin cewa an faro shine a shekarar 1902, kuma wancan lokacin Barcelona ce ta fara samun nasara kan Madrid da ci 3-1. Sai dai a wasan na daren jiya Lahadi Madrid ce ta samu nasara da ci 2-1. Sakamakon wannan wasa ya bada mamaki matuƙa, domin dai an yi tunanin Barcelona za ta yi wa Madrid Kukkunge ne, kasancewar tana gida tare da goyon bayan mutane dubu 62,650 da suka taru a filin wasan Spotify Camp Nou, domin ganin yadda zata kaya. Haka nan ƙungiyar ta kwashe sama da shekara guda ba tare da tayi rashin nasara a filin ba, domin rashin nasara ta ƙarshe da tayi a nan ita ce a hannun Villarreal a ranar 18 ga watan Mayun shekarar bara, gashi kuma tayi nasara a wasanni 6 cikin 7 na haɗuwarsu. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............

26 Okt. 2026
684-

Nasarar tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Najeriya akan Comoros

Shirin 'Duniya Wasanni' a wanan mako tare da Khamis Saleh zai dubu ne kan nasarar da tawagar Super Falcons ta samu kan Comoros, inda a makon da ya gabata ne aka kammala wasa na biyu na zagaye na biyu na neman zuwa gasar Olympics da aka yi tsakanin tawagar mata ta Super Falcons ta Najeriya da takwararta ta Coromos. An dai buga dukkanin wasanni biyu ne a filin wasa na Remon Star da ke garin Ikenne na jihar Ogun, inda a wasan farko Super Falcons ta samu nasara da ci 2 da nemam sannan a wasa na biyu aka tashi 5 da nema, a jumlace gida da waje Najeriya ta jefa kwallaye biyar da nema a ragar Comoros.

19 Okt. 2026
683-

Messi ya yi bankwana da tawagar Argentina bayan doka wasanni 208

Shirin "Duniyar Wasanni" tare da Khamis Saleh a wannan mako, zai dubu ne kan bankwanan da Lionel Messi ya yi da tawagar Argentina. A farkon watan Oktoban nan da muke ciki ne kyaftin ɗin tawagar ƙasar Argentina Lionel Messi, yayi bankwana da tawagar bayan kwashe tsawon shekaru 21 tana wakiltar ƙasar a wasannin matakin ƙasa da ƙasa. Messi ya fara bugawa Argentina wasanni ne a ranar 17 ga watan Agustan shekarar 2005 a wani wasan sada zumunci da suka yi da Hungry, inda ya samu nasarar buga wasanni 208, kafin murabus ɗinsa a ƙarawarsu da Benin a ranar 7 ga watan Oktoban shekarar 2026. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin..

12 Okt. 2026
682-

Yadda ƴan wasa ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin hutu

Shirin a wannan mako ya yi duba ne kan yadda ƴan wasan da ke taka leda ke dawowa gida don buga wasannin sada zumunci a lokacin da suke hutu. A duk lokacin da aka kammala wasannin lig-lig a kan tafi hutu a kowace shekara musamman a nahiyar Turai da lig ɗin su ya fi jan hankali, wanda hakan kuma ke buɗe wani babi na wasanni a yankuna daban-daban da ƴan wasan ke fitowa domin nuna bajintarsu a zahiri a wasannin sada zumunta da a ke shirya musu. Latsa alamar sauti don sauraren shirin...

05 Okt. 2026